in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar "kyakkyawan karfi" wajen bunkasa sabuwar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka
2014-04-26 16:26:13 cri
A Asabar 25 ga wata, jakadan kasar Sin dake kasar Amurka mista Cui Tiankai ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ake kokarin bunkasa sabuwar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka shi ne cimma burin neman samun ci gaba tare bisa ka'idar girmamawa juna. Sakamakon haka, ana bukatar "kyakkyawan karfi" wajen kokarin cimma burin tare.

Mista Cui ya fadi haka ne a yayin da yake jawabi a kwalejin hukuma ta Kennedy ta jami'ar Harvard ta kasar Amurka. Cui Tiankai ya kuma nuna cewa, kasar Sin na kokarin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman bunkasuwa da bude kofa a yankin Pacifik da na Asiya bai daya. Neman raba wannan yankin da ya zama wasu kungiyoyi masu adawa da juna ko kafa kawance daban daban a yankin, ba matakin da ya dace ba ne.

Mr. Cui Tiankai ya kara da cewa, bangaren Sin ya riga ya bayyana matsayin da ya dauka a bayyane sosai kan batun tsibirin Diaoyu, wato tsibirin shi ne yankin kasar Sin tun fil azal. Ya kuma bayyana cewa, yarjejeniyar kare juna da aka kulla tsakanin kasashen Amurka da Japan yarjejeniya ce da ya kamata ta yi tasiri ga bangarorin biyu kawai, bai kamata ta kawo illa ga moriyar bangare na wani daban ba, balle yankin kasar Sin.

Sannan Mr. Cui Tiankai ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta ji tsoron kowace irin barzanar da za a yi mata ba, kuma ba za ta janye jikinta kan kare babbar ka'ida ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China