A cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, an kulla dankon zumunci a tsakanin Sin da Tanzaniya. Don haka su aminai ne a ko da yaushe. Shugaba Xi ya ce, ya mai da hankali kan raya huldar da ke tsakanin Sin da Tanzaniya, sa'an nan yana son yin kokari tare da shugaba Kikwete wajen kara azama kan bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon matsayi.
Shi ma a cikin sakonsa, shugaba Kikwete ya ce, huldar da ke tsakanin kasarsa da Sin ta sha bamban da saura. Ya lura da cewa, kasashen 2 aminai ne a ko da yaushe. Don haka yana son sake nanata cewa, gwamnatinsa za ta himmantu wajen kara inganta kyakkyawar huldar abokantaka da hadin gwiwa a taksanin kasashen 2, a kokarin kawo alheri ga jama'ar kasashen 2. (Tasallah)