A yayin ganawar, mista Li ya ce, Sin da Tanzaniya sun kulla dankon zumunci a tsakaninsu, kuma su aminai ne a ko da yaushe. Kasar Sin na fatan aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma daga dukkan fannoni ta hanyar amfani da damar cikon shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, tare da zurfafa kyakkyawar hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, a kokarin raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni domin samun moriyar juna da nasara tare da kuma kawo wa jama'arsu alheri.
A nasa bangaren kuma, mista Membe ya ce, kasarsa ta darajta dadadden zumunci da ke tsakaninta da Sin, don haka tana son himmantuwa wajen kara habaka hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban.(Tasallah)