in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Tanzaniya
2014-02-26 10:42:49 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Tanzaniya Bernard Kamillius Membe a nan birnin Beijing ranar Talata 25 ga wata.

Yayin ganawarsu, minista Wang Yi ya ce, huldar diplomasiyyar shekaru 50 dake wanzuwa tsakanin Tanzaniya da Sin ta samu ci gaba matuka. Ya ce, har kullum kasashen 2 na nunawa juna goyon baya da aminci a ko da yaushe. A bana da ake murnar cika shekaru 50 da kulla hulda tsakanin kasashen 2, kasar Sin na fatan amfani da wannan dama, domin kara cudanya tsakanin manyan jami'an gwamnatocin 2, tare da daga matsayin hadin gwiwarsu, ta yadda za a ciyar da huldar dake tsakanin su, da moriyar juna zuwa mataki na gaba.

Wang Yi ya kara da cewa, dandalin hadin kan kasashen Sin da Afirka, wani tsari ne mai amfani a fannin kara musayar ra'ayi, da hadin kai tsakanin Sin da Afirka. Don haka kamata ya yi bangarorin 2 su yi kokari tare don taimakawa kokarin kara kyautata tsarin.

A nasa bangaren, Bernard Membe, cewa ya yi, kasar Sin sahihiyar aminiya ce ta kasashe masu tasowa, wadda ta kan tallafawa kasashen Afirka, ciki har da Tanzaniya, a kokarinsu na raya tattalin arziki. Don haka Tanzaniya tana alfahirin ganin kasacewar ta abokiyar hulda da kasar Sin, tare da fatan samun ci gaba kan hadin kan kasashen 2 a fannoni daban daban. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China