in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MDD ya nada sabon wakili na musamman kan samar da kudaden yaki da cutar malaria da cimma manufofin kiwon lafiya
2013-03-02 16:46:50 cri
Magatakardan MDD Ban Ki Moon ya sanar da nada Ray Chambers ranar Jumma'a a matsayin wakili na musamman na samo kudaden yaki da cutar malariya da ma sauran harkokin bunkasa kiwon lafiya na muradun karni, wato matakan nan guda 8 da aka maida hankali kansu don yaki da talauci nan da shekara ta 2015.

Chambers wanda dan kasar Amurka ne, shi ne ke kan matsayin wakilin musamman na babban sakataren kan yaki da cutar malaria tun cikin watan Fabrairun shekarar 2008, in ji sanarwa da mai magana da yawun magatakardan ya bayar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa a matsayinsa na maida hankali kan batun kudade, Mr Chambers zai yi hadin gwiwa da cibiyoyin MDD, da shirye shirye da ma samar da kudade don bunkasawa da kuma ganin kafofi na gwamnati da masu zaman kansu sun ba da kudade don a samu cimma buri a fuskar kiwon lafiya na muradin karnin musamman a fannin mutuwar yara da mata masu juna biyu, yaki da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro, tarin fuka da dai sauran cututtuka.

A lokacinda Mr Chambers ke kan matsayin wakilin musamman na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, an yi nasarar tara kudade sama da dalar Amurka biliyan 4, sannan an raba ragar kama sauro guda miliyan 400 da kuma gabatar da sauran matakan bada magunguna.

Duk da wadannan nasarori, har yanzu cutar ta cizon sauro tana kashe yaro daya a Afirka cikin kowanne sekon 45, in ji sanarwar.

Idan aka kara jan damara, za'a iya kusan kawar da yawan masu mutuwa nan da shekarar 2015, ganin cewa babban kalubale a yanzu shi ne na rashin isassun kudaden cimma bukatun kiwon lafiya a kasashe da dama. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China