A ranar 19 ga wata, majalisar dinkin duniya ta yi taron manyan jami'ai kan batun rigakafi da kuma shawo kan cututtuka marasa yaduwa a hedkwatarsa wato birnin New York na kasar Amurka. A yayin taron, babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya kirayi kasa da kasa da su kara mai da hankali kan wannan batu kuma su dauki matakan da suka dace domin ceton rayukan jama'a. Ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu shi ma ya yi jawabi a yayin taron inda ya gabatar da shawarwari uku game da yadda za a yaki da kalubalen da ya zo daga cututtuka marasa yaduwa ga kasashen duniya, a sa'i daya kuma, ya yi bayani kan matakan da kasar Sin ta dauka a wannan fanni a halin yanzu.(Jamila)