in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a hada kai domin kawar da ciwon fukka a duniya
2014-03-25 11:01:28 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira a ranar Litinin da a karfafa taimakon kasa da kasa domin kawar da ciwon tarin fukka (TB), musammun ma ta hanyar tattara kudade domin cike gibin kudin da ake da su wajen samar da jinya da kuma yaki da ciwon tarin fukka.

Ta hanyar ba da jinya ga mutane miliyan uku da ba su samun kulawar da suke bukata, za'a yi kokarin kyautata makoma mai haske ga duniya baki daya, in ji shugaban MDD a cikin wata sanarwa da ya yi albarkacin ranar duniya ta yaki da ciwon tarin fukka.

Mista Ban ya tunatar da cewa, ciwon tarin fukka na a sahu na biyu cikin cututtuka masu yaduwa da suka fi kashe mutane a tsakanin baligai, bayan cutar Sida, kuma a kowace shekara, cutar na kashe mutane miliyan 1,3 a duniya a yayin da kusan miliyan 9 suke fama da sauran cututtuka.

A cewar mista Ban Ki-moon, babban adadin masu jinya ya fi shafar bangaren matalauta, misalin ma'aikata 'yan-ci-rani, 'yan gudun hijira da mutanen da aka gusa, fursunoni, kananan kabilu da mutanen karkara.

Sakamakon cigaban da aka samu a 'yan shekarun baya bayan nan ya nuna cewa, akwai damar a fuskanci wannan barazana ta hanyar yawaita ayyukan hadin gwiwa.

Tsakanin shekarar 1995 da shekarar 2012, gudanar da ayyukan kiwon lafiya a fadin duniya ya taimaka wajen ceton mutane miliyan 22 da kuma samar da jinya ga mutane miliyan 56 dake fama ciwon tarin fukka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China