Ranar 17 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta gabatar da wani rahoto mai taken "Halin da duniya ke ciki a shekarar 2012 a fannin rigakafin zazzabin cizon sauro", wanda ya nuna cewa, daga shekarar 2010 zuwa 2012, ana fuskantar koma baya a fannin rigakafin zazzabin cizon sauro, sakamakon rashin samun tallafin isassun kudade.
Rahoton ya yi kiyasin cewa, za a bukaci kudi kimanin dalar Amurka biliyan 5.1 a kowace shekara, daga shekarar 2010 zuwa 2020 a wannan fanni, amma yawan kudin da aka samu a shekarar 2011 bai wuce dala biliyan 2.3 ba, ban da haka, yawan magungunan rigakafi da aka samar ga kasashen da cutar zazzabin cizon sauro ke yaduwa ya ragu matuka.
Dadin dadawa, rahoton ya ce, wasu kalubalolin da ake fuskantar ciki hadda rashin samun isassun kudaden na kawo babbar illa ga aikin yin rigakafin cutar. An ce duk da hakan an samu ci gaba mai armashi a wannan fanni daga shekarar 2001 zuwa 2010, inda yawan mutuwar masu cutar ya ragu da kashi 26 bisa dari, kuma an kare mutanen da yawansu ya kai miliyan 270 daga kamuwa da wannan cuta sakamakon taimakon da aka bayar, yayin da wasu miliyan 1.1 suka samu damar waraka, sakamakon aikin jiyya da suka samu bayan sun kamu da cutar. (Amina)