Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanawar hutu bikin Easter tun daga yau ranar Jumma'a 18 ga wata har zuwa ranar Litinin 21 ga wata, dalilin haka ne gwamnatin Amurka ta jawo hankalin al'ummarta da suke zaune a kasar dasu kiyaye kansu.
Gwamnatin Amurka ta ci gaba da jan hankalin al'ummarta da su yi kaffa-kaffa a wuraren ibada da sauran wasu wuraren dake dauke da cunkoson jama'a a yayin bikin na Easter.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.