Wata sanarwa da ta fito daga ofishin na UNMISS ta ce, rahoton wanda tuni aka mika shi ga kwamitin sulhun MDD, ya kunshi bayanai kan zargin kisan fararen hula, da amfani da karfin tuwo, tare da keta alfarmar wasu al'ummu bisa dalilai na kabilanci.
A cewar rahoton, tsakanin 15 ga watan Disambar bara zuwa watan Janairun nan da muke ciki, al'ummun jahohin Jonglei, da tsakiyar Equatoriya, da Unity da kuma jihar Upper Nile, na cikin wadanda wannan balahira ta fi shafa.
Bugu da kari, ofishin na UNMISS ya ce zai fidda wani cikakken rahoto, don gane da halin da ake ciki a kasar ta Sudan ta kudu, musamman kan batun keta hakkin bil Adama, a cikin watan Afirilu mai zuwa. (Saminu Alhassan Usman)