Veitch ya ce kasar Sudan ta kudu na sahun gaba a jerin kasashen da yara ke fuskantar karanci abinci mai gina jiki, inda kimanin yara 250,000 ke fuskantar barazanar hakan, nan da karshen wannan shekara da muke ciki.
Wakilin asusun na UNICEF ya alakanta wannan barazana da yaran kasar ke ciki, da rashin damar gudanar da aikin noma yadda ya kamata, sakamakon tashe-tashen hankulan dake addabar kasar. Ya ce tuni wani kaso mai yawa, na yaran kasar suka fada wannan layi na kamfar abinci mai gina jiki, cikin shekaru 2 da rabi da kasar ta shafe bayan samun 'yancin kai a shekarar 2011.
Har wa yau Veitch ya jaddada muhimmanci daukar matakan gaggawa, domin kaucewa rasa rayukan yara kimanin 500,000, wadanda ya ce na iya rasuwa muddin ba a hanzarta kaiwa kasar dauki ba.(Saminu Alhassan)