An jiyo amon wani abu da ake zaton mai yiwuwa ne ya kasance daga na'urar nadar bayanan jirgin nan ne da ya bace
Babban jami'in cibiyar kasar Australiya mai kula da ayyukan neman jirgin saman kasar Malaysiyan nan da ya bace mai lambar MH370 Angus Houston ya ce, baya ga amon wani abu da ake zaton mai yiwuwa ya kasance daga na'urar nadar bayanan jirgin, wanda wani jirgin ruwan kasar Sin ya jiyo, bangaren Australia ma ya jiyo wani amo na daban. Kuma yanzu sassa daban daban da ke aikin laluben jirgin cikin hadin gwiwa na ci gaba da gudanar da bincike a wadannan wurare 2 da aka jiyo amon.
Mista Houston, wanda ya bayyana hakan a yau Lahadi ya ce, abin da jirgin ruwan kasar Sin ya jiyo yana da muhimmanci sosai kuma ya faranta rayukan mutane.
Ya kara da cewa, bisa amon guda 2 da aka jiyo, ga alama an dauki matakin da ya dace na gudanar da ayyukan laluben a kudancin yankin tekun na Indiya. (Tasallah)