A daren ranar 14 ga wata ne dai wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai 'yan mata sama da 100, daga kwalejin ta garin Chibok. A kuma halin yanzu, sojojin Nijeriya na yunkurin ceto sauran daliban da ake zaton suka hannun maharani.
Ko da yake babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin lamarin, a hannu guda 'yan sanda da wasu kafofin watsa labarai a jihar, suna zargin 'yan Boko Haram ne suka aikata hakan.
Don gane aukuwar lamarin, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya fidda wata sanarwa a ran Laraba, inda ya yi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai makarantar, ya kuma bukaci da aka kubutar da daliban cikin sauri don su koma gidajensu.
Cikin sanarwar, Mr. Ban ya kuma nuna damuwarsa game da hare-haren da ake kaiwa wasu makarantun dake arewacin Nijeriya, ya kuma jaddada cewa hare-haren da ake kaiwa makarantun sun yi matukar sabawa dokokin jin kai na kasa da kasa.
Bugu da kari, Mr. Ban ya ce kamata ya yi a kiyaye tsaron makarantu yadda ya kamata, ta yadda dalibai za su samu damar karatu cikin kwanciyar hankali. (Maryam)