A cikin wata sanarwa da aka aika wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin bai ba da adadin yawan mutanen da suka mutu ba, amma wasu da lamarin ya abku gaban idonsu sun ce, mutane sama da goma sun mutu.
Sai dai mista Dole ya ce, an kama wani mutumin da ake zargi, kuma tuni manjo janar Junaid Bindawa, babban ofisa na rundunar sojojin jihar ya ba da umurnin gudanar da bincike mai zurfi kan wannan lamarin.
Harin dai ya abku lokacin ranar hutu ta kasa domin tunawa da haifuwar manzon Allah, kuma muhimmin lokaci ne da mutane suke gudanar da harkokin kasuwanci sosai.
Jihar Borno na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram tun daga shekarar 2009, a lokacin da kungiyar ta fara kai hare-harenta kan gine-ginen kristoci, gine-ginen jami'an tsaro, makarantu da kauyuka. (Maman Ada)