in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 40 sun rasu a sanadiyyar hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Borno ta Nijeriya
2013-08-13 10:28:10 cri
Ran 11 ga wata, 'yan bindiga sun kai farmaki a unguwannin Konduga da Mafa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar Nijeriya, inda a kalla mutane 40 suka rasu, yayin da guda 25 suka jikkata a sanadiyyar harin.

Ran 12 ga wata, wani jami'in hukumar kafa doka ta unguwar Konduga ta jihar Borno Ali Bukar Dalori ya bayyana cewa, mutane da dama sun rasu ko jikkata a sanadiyyar harin, kana a halin yanzu, an riga an kai wadanda suka ji rauni zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri don ba da jiyya gare su, amma bai yi karin bayani kan lamarin ba, kuma bai nuna adadin mutane wadanda suka rasu ko jikkata yayin rikicin ba.

Amma, wani ma'aikacin asibitin ya nuna cewa, a kalla mutane 40 sun rasa rayukansu yayin rikicin, kuma a halin yanzu wadanda suka ji rauni sama da guda 25 suna karbar jinya a asibitin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China