Mutanen da suka mutu sakamakon harin da aka kai a jihar Bornon Nigeriya sun kai 85.
A jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriya, adadin wadanda suka halaka sanadiyar harin da wassu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne ya kai 85 bayan da aka sake gano gawawwaki a wassu wurare, in ji wani jami'in jihar a ranar talatan nan.
Maharan sun kai harin ne kwanaki biyu da suka gabata a kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga mai nisan kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar na Borno.
Sakataren karamar hukumar ta Konduga Ali Kaka Yale ya ce, ya zuwa lokacin da yake bayani ga manema labarai an samu gawawwaki guda 85 kuma har yanzu ba'a ga wassu mutane 16 ba.