YA yau Laraba 16 ga wata, a gun taron manema labaru, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta bayyana kan batun kai hari kan wata makarantar Nijeriya cewa, Sin ta yi zargi kanAllah wadai da kowane irin matakin ta'addanci da babbar murya. Gwamnatin Sin ta yi kira da a saki daliban da aka yi garkuwa da su nan take, tare da tabbatar da tsaronsu yadda ya kamata. A matsayin aminiyar hadin gwiwa ta Nijeriya bisa manyan tsare-tsare, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi na a fannin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Fatima)