in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an diplomasiyya na Tanzaniya da Afrika ta kudu na sa ran alheri ga ziyarar shugaban kasar Sin a Afrika
2013-03-19 14:39:58 cri

A ranar 18 ga wata jami'an diplomasiyya na Tanzaniya da Afrika ta kudu dake kasar Sin a nan birnin Beijing, suka nuna kyakkywan fata dangane da ziyarar da shugaban kasar Sin, Xi Jinping zai kai Afrika.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta sanar a wannan rana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara wasu kasashe daga ran 22 zuwa 30 ga wata bisa gayyatar da aka yi masa.

Kasashen da zai ziyarta sun hada da Rasha, Tanzaniya, Afrika ta kudu,da Jamhuriyyar dimukradiyyar Kongo, kuma Xi zai halarci taron shugabannin kasashen BRICS karo na biyar.

Wannan shi ne zai kasance ziyarar aiki karo na farko na Xi, bayan ya hau kan mukamin shugaban kasar Sin.

Jakadan Tanzaniya dake kasar Sin Philip Sang'ka Marmo ya nuna cewa, ziyarar da Xi zai kai za ta taimaka wajen kara sada zumunci tsakanin kasashen biyu, kuma ana sa ran kasashen biyu za su kulla yarjejeniyar hadin kai a fannoni daban-daban ciki hadda noma, sha'anin masana'antu, makamashi, manyan kayayyakin more rayuwa da sauransu.

Mashawarci a sashin kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Afrika ta kudu dake kasar Sin Guo Yi ya nuna cewa, akwai babbar ma'ana dangane da ziyarar ta Xi Jinping.

Wannan shi ne karo na biyu da Xi zai kai ziyara a kasar bayan shekarar 2010. Ziyarar tasa a wannan karo za ta taimakawa kamfanonin kasashen biyu da kuma sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu, har ma da samar da sharadi mai kyau ga hadin gwiwa da kasashen biyu za su yi nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China