in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata bangarorin da batun Ukraine ya shafa su kai zuciya nesa
2014-03-28 20:40:46 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ran 28 ga wata cewa, ya kamata bangarorin da batun Ukraine ya shafa su kai zuciya nesa, kada su dauki matakan da za su kawo karin barazana ga batun kasar Ukraine, da kuma kara rikice-rikicen dake tsakanin bangarorin da abin ya shafa, wajibi ne a samar da kyakkyawan yanayi wajen warware rikicin kasar ta hanyar siyasa.

A daren ranar Alhamis 27 ga wata,aka kada kuri'u kan daftarin kudurin batun Ukraine a babban taron MDD, inda kasar Sin ta janye daga jefa kuri'a.

Dangane da haka, Hong Lei ya bayyana a wajen taron manema labaran da a yau Jumma'a cewa, batun Ukraine ya shafi hankula da kuma moriyar bangarori daban daban, don haka ya kamata a yi la'akari da moriyar bangarori daban daban wajen warware batun.

Haka kuma in ji Mr Hong, muhimmin aiki a halin yanzu shi ne, a sassauta yanayin kasar Ukraine, tare da kawar da sabani ta hanyar yin shawarwari, a kokarin cimma matsayi daya kan batun, ta yadda za a iya warware batun a siyasance. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China