Bisa labarin da ofishin ba da umurni ga jirgin ruwa mai suna 'Haixun 01' na nan kasar Sin ya fitar a yau Laraba, yankin da jiragen Sin ke gudanar da laluben jirgin sama kasar ta Malaysia nan da ya bace, ya kai fadin muraba'in kilomita dubu 220, daga arewa maso gabashin gabar ruwan kasar Australiya. Cikin fadin muraba'in kilomita miliyan 1 da dubu 150, na daukacin yankin tekun na Australiya dake Arewa maso gabashin yankin tekun da aka gudanar da aiki a jiya Talata.
Ban da wannan kuma. Cibiyar kula da aikin ceto a tekun kasar Australiya, ta riga ta mika dukkan aikin ceton ga ma'aikatar tsaron kasar, inda hukumar kula da harkokin teku ta kasar Australiyan ta karbi daidaita tsarin aikin tsakanin kasashen da abin ya shafa. (Danladi)