in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta karfafa hadin gwiwar aikin teku da na sama wajen binciken jirgin saman Malaysian da ya bace
2014-04-04 10:32:05 cri
A ran 3 ga watan Afrilu, jiragen ruwa da na sama na kasashen Sin da Australia sun ci gaba da neman jirgin saman Malaysian da ya bace a kudancin tekun India, amma ya zuwa yanzu, ba a samu muhimmin ci gaba kan aikin ba.

Firaministan kasar Australia Tony Abbott ya bayyana cewa, ko da yake aikin neman jirgin saman nan ya kasance mafi wuya cikin tarihin dan Adam, kasar Australia za ta ci gaba da kokarinta, ba za ta bata wa iyalan fasinjojin jirgin rai ba.

Bisa bayanin da hukumar musamman game da aikin ceto ta kasar Australia ta fidda a ran 3 ga wata, an ce, a wannan rana, gaba daya akwai jiragen sama guda 10, da jiragen ruwa guda 9 da suka gudanar da aikin bincike a kudancin tekun India, dake da nisan kilomita 1680 da yammacin birnin Perth na kasar Australia, kuma muraba'in yankin da aikin ya shafa ya kai kilomita dubu 223.

Bugu da kari, a wannan rana firaministan kasar Malaysia Najib Razak tun da ya isa birnin Perth, ya tabbatar wa iyalan fasinjojin jirgin saman da ya bace cewa, kasar Malaysia za ta ci gaba da aikin neman jirgin, har sai ta gano inda jirgin yake.

Kuma bisa bayanin da cibiyar aikin ceto kan teku ta kasar Sin ta yi a jiya Alhamis, an ce, tun bacewar jirgin saman Malaysia ya zuwa yanzu, gaba daya kasar Sin ta aike da jiragen ruwa guda 18 tare da jiragen sama guda 11 wajen gudanar da aikin bincike, , kuma akwai jiragen ruwan kasuwanci sama da 60, da jiragen ruwan aikin su sama da 20 da suka ba da taimako kan aikin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China