Har wa yau an ce, yawan mutanen da bala'in ya shafa ya haura dubu 68. Baya ga gidaje da dama da suka rushe, har wa yau, da dama daga na'urorin samar da ruwa, da na wutar lantarki, da sadarwa da dai sauransu, su ma sun lalace.
Ya zuwa safiyar yau Lahadi, gwamantin lardin nan na Yunnan ta tsai da kudurin samar da yuan miliyan 3, domin gudanar da aikin ba da agaji. Tuni kuma aka dawo da ayyukan sufuri, da wutar lantarki, da kuma na sadarwa a sassan yankin da bala'in ya auku.
Bayan girgizar kasar da ta faru a gundumar Yongshan, hukumomin da abin ya shafa sun aike da masana 80, don gudanar da bincike kan illar da girgizar kasar ta haddasa wa yankin, kuma masanan za su sa ido kan yanayin da yankin ke ciki, domin magance karin bala'un da girgizar kasar ka iya haifawa.(Maryam)