Hakazalika bala'in ya janyo asarar dukiyoyin jama'a da muhalli inda ya lalata dakuna 2731, yayin da wasu 75 suka rubta gaba daya. Haka kuma girgizar kasar ta lalata makarantu dake gundumomi 6. Hukumomin gudumar sun tabbatar da cewa y an riga an maido da wutar lantarki, sufuri da kuma sadarwa a yayin da kuma aka kebe tantuna 650 zuwa yankin dake fama da bala'in, tare da tsugunar da mutane dubu 21 cikin gaggawa.(Fatima)