Hukumomin sun kuma sanar da aikewa da wasu kungiyoyi yankuna masu fama da laba'in girgizar kasa, don gudanar da bincike kan yanayin da yankunan ke ciki, da kuma bada jagoranci ga aikin ba da agaji.
Bisa rahotannin da hukumar kula da harkokin jama'ar lardin Yunnan, da ta lardin Sichuan suka bayar, an ce, da misalin karfe 8 da minti 4 na wannan rana ne, wata girgizar kasa mai karfin maki 5.9 ta auku a yankin iyakar garin Derong dake karamin yanki mai cin gashin kansa na kabilar Tibet da ke lardin Sichuan, da kuma garurruwan Dexin, da Shangri-La, na karamin yanki mai cin gashin kansa na kabilar Tibet da ke lardin Yunnan.
Kuma bisa kididdigar rikon kwarya da aka yi, mutane guda 4 ne suka rasu sakamakon aukuwar wannan lamari, yayin da kuma wasu mutane 13 suka jikkata.
Bayan faruwar wannan lamari, shi ma kwamitin ba da agaji ga mutanen da laba'i ya aukawa na lardin Yunnan, da kuma hukumar kula da harkokin jama'ar lardin, sun sanar da daukan matakan ba da agaji ga yankunan, kuma sun aike da kungiyoyin ba da agaji zuwa yankuna masu fama da bala'in.
Haka kuma hukumomin biyu na lardin Sichuan, sun sanar da daukan matakan ba da agaji gaggawa ga yankunan, sun kuma aike da jami'ai zuwa wadannan yankuna domin kara tantance halin da ake ciki. (Maryam)