in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin tsaron Amurka zai kawo ziyara kasar Sin
2014-04-04 16:34:43 cri
A ran 3 ga wata, ministan harkokin tsaron kasar Amurka Chuck Hagel ya bayyana a Hawaii cewa, kasar Amurka na son karfafa hadin gwiwarta tare da kasar Sin, da kuma yin musayar ra'ayi kan wasu manyan bututuwan da suke fama da sabanin ra'ayi a kansu.

Bisa goron gayyatar da wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kuma ministan harkokin tsaron kasar Chang Wanquan ya ba shi, Mr. Hagel zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin tun daga ranar 7 har zuwa ranar 10 ga wata. Wannan ita ce ziyara ta farko da jami'in zai kawo Sin, tun bayan da ya kama wannan mukami.

A yayin taron manema labaran da aka yi bayan aka kammala taron kara wa juna sani tsakanin Amurka da kungiyar tarayyar kasashen Asiya ta kudu maso gabas kan harkokakin tsaro a ran 3 ga wata, mista Hagel ya bayyana cewa, zai gana da shugabannin kasar Sin yayin ziyarar da zai kawo domin ingiza ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yin musayar ra'ayi kan wasu manyan bututuwan da suka fi janyo hankalin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China