in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka
2013-04-13 19:10:35 cri

A yau Asabar ne Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry wanda ke ziyara a kasar, don tattaunwa kan dangantaka tasakaninsu da sauran batutuwan dake jan hankulansu.

Xi ya bayyana Kerry a matsayin gogaggen jakadan Amurka tare da karin cewa yana mai gamsuwa kan yadda Kerry ke dagewa a fuskar bunkasa dangantaka tsakanin Amurka da kasar Sin.

Ya ci gaba da cewa wannan ganawa na nuna irin muhimmanci da kasashen biyu ke dorawa kan dangantaka tsakanin kasar Sin da Amurka.

Shugaba Xi ya ce dangantaka tsakanin Amurka da Sin tana cikin kyakkyawan yanayi, inda har ya tabo tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da shugaba Barack Obama a ranar da aka zabe shi. Shugaba Xi tare da jaddada dagewarsu na samun bunkasar dangantaka tasakanin Sin da Amurka.

Xi ya ce yana fata wannan ziyara da Kerry ya kawo wacce ita ce ta farko zuwa kasar Sin bayan hawarsa wannan mukami a cikin watan Fabrairu, za ta kara zammar bunkasa dangantakarsu.

A nasa bangare sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana cewa ko shakka babu ana cikin wani muhimmin lokaci ne da ake fuskantar dimbin kalubale, inda ya tabo batutuwa kamar na yankin Koriya, batun makaman nukiliya a kasar Iran, batun kasar Syria da yankin gabas ta tsakiya har ma da batun tattalin arziki a fadin duniya dake bukatar samun bunkasa. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China