Jaridar Washellongton Post ta bayar da labari a shafinta na Internet cewa, kasar Sin ta yi kira da a yi shawarwari don warware halin kunci a zirin Koriya cikin ruwan sanyi, kana kuma jaridar New York Times ta ba da labari cewa, Kerry ya ce, idan Koriya ta Arewa ta yi watsi da shirin makaman nukiliya, kila ne, Amurka za ta rage tsarin kakkabo makamai masu linzami.
Ban da wannan kuma, kamfanin dillancin labaru na AFP da na kasashen Japan da Koriya ta Kudu sun bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka sun amince da kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya cikin lumana.
A yayin ziyarar Kerry a kasar Sin, kasashen Sin da Amurka sun tattauna batun sauyin yanayi, da tsaron yanar gizo ta Internet. Bugu da kari kuma, a cikin bayanin da kamfanin dillancin labaru na Reuters da na AFP suka bayar, an ce, kasashen Sin da Amurka sun bayyana cewa, ya zama dole a inganta tsaron yanar gizo ta Internet da batun sauyin yanayi a duniya, don haka za a kafa wani rukunin daidaita batun tsaron yanar gizo da wani na daban don tabbatar da batun sauyin yanayi na duniya.(Bako)