in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gabatar da shawarwarin daidaita matsalar Ukraine
2014-03-27 11:06:49 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Hong Lei, ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda 3,wadanda zasu taimaka wajen daidaita matsalar siyasar kasar Ukraine.

Mr. Hong ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka shirya a ran 26 ga watan nan. Har wa yau ya ce kan batun yin gyare-gyare a huldar kasa da kasa game da asusun ba da lamuni na IMF, kasar Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa, da su sa kaimi ga majalisunsu don amincewa da kuduri masu alaka da hakan.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labru, Mista Hong ya ce kasar Sin tana rike da matsayinta na adalci, da lura da hakikanin matsalar Ukraine.

Haka nan shawarwari Uku da Sin ta gabatar sun hada gaggauta kafa wani tsari da zai hada bangarori daban daban wajen guda, domin tattaunawa da neman hanyar da ta dace, wajen daidaita matsalar kasar a siyasance. Sai bukatar bangarorin da abin ya shafa, su kaucewa daukar matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki yayin da ake tsaka da tattaunawa. Shawar ta Uku kuwa ita ce bukatar da ake da ita ga hukumomin duniya, ta yin nazari, domin ba da taimako ga Ukraine, wajen kiyaye zaman lafiya a fannonin tattalin arziki da kudi.

Kasar Sin na fatan kasashen da abin ya shafa za su yi kokari wajen cimma wadannan burika.

Hong ya ci gaba da cewa, a kan batun yin gyare-gyare a huldar kasa da kasa game da asusun ba da lamuni na IMF, kasar Sin tana rike da matsayinta na zahiri. Inda ta bukaci kasashen da abin ya shafa su sa kaimi ga majalisunsu domin amince da kudurin da suka jibanci wannan lamari, ta yadda za a iya aiwatar da kudurorin da aka riga aka zartas a IMF yadda ya kamata. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China