Yayin ganawarsu, Mr. Zhang ya bayyana cewa, shekarar bana ita ce cikon shekaru 30 da aka kulla dangantakar diplomasiya tsakanin kasar Sin da kasar Cote d'Ivoire, kasar Sin na mai da hankali sosai wajen raya dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu, kuma tana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Cote d'Ivoire wajen karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya don neman ci gaba tare.
Ya kara da cewa, ayyukan da suka shafi yin gyare-gyare a kasa da Sin ta gabatar yayin cikakken zaman taro na 3 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 18 za su kawo wa kasashen biyu sabuwar dama wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakaninsu kan fannoni daban daban.
A jawabinsa Mr. Soro ya bayyana cewa, kasar Sin abokiyar arzikin kasar Cote d'Ivoire ce, kasar tana son ci gaba da karfafa dangantakar abokantaka da ke tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, da kuma koyon fasahohin kasar Sin wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'ummar kasa. (Maryam)