Kakakin kungiyar likitocin ba da agaji ta kasa da kasa Mariano Lugli, wanda a halin yanzu ke kula da aikin hana yaduwar cutar ta Ebola a kasar Guinea, ya bayyana a jiya Litinin cewa, cutar ta Ebola na yaduwa cikin sauri, kuma cikin dan lokaci kadan, ta yadu daga gandun dajin kudu maso gabashin kasar ta Guinea, zuwa babban birnin kasar dake da nisan darurruwan kilomita daga inda aka fara samun bullarta, ya zuwa kasashen dake makwabta da ita.
A dai wannan rana, ita ma gwamnatin kasar Libya ta tabbatar da cewa, cutar Ebola ta riga ta yadu zuwa kasar, yayin da ita ma kasar Senegal, dake makwabtaka da Guinea ta sanar da rufe sassan kan iyakarta da Guinea.
A farkon watan Fabrairun da ya shude ne dai aka fara samun barkewar cutar a kasar Guinea, aka kuma tabbatar da cewa, Ebola ce, a ran 22 ga watan Maris. Ya zuwa yanzu kuwa, cutar ta riga ta hallaka mutane 78. Wannan shi ne karo na farko da aka samu barkewar cutar Ebola a yankuna masu yawa a yammacin Afirka. (Maryam)