in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane goma suka kamu da cutar Ebola daga cikinsu bakwai sun mutu zuwa ranar Juma'a a Guinee
2014-03-29 17:02:41 cri
Kasar Guinee ta gano tun ranar Jumma'a 28 ga wata, da wasu sabbin mutane goma da suka kamu da cutar dake haddasa zubar da jini wato Ebola, a yayin mutane bakwai daga cikinsu suka mutu, lamarin da ya kai ga yawan mutane da suka kamu da cutar zuwa 112, tare da mutuwar mutane 70 tun bayan bayan barkewar wannan annoba mai kashewa, in ji ministan kiwon lafiya na kasar Guinee.

Gundumar Guekedou dake kudancin kasar da aka fara gano da wannan cuta ya zuwa yanzu na da mutane 73 da suka kamu da wannan cuta da mutuwar mutane 51, sannan gundumar Macenta tana da masu cutar 22 da mutane 12 da suka kwanta dama, gundumar Kissidougou mutane 7 da suka kamu da cutar da mutum biyar suka mutu, a Dalaba an gano mutum guda da ya kamu da cutar da mutuwar mutum daya sannan Conakry babban birnin kasar an gano mutane 8 da suka kamu da cutar da mutuwar mutum daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China