Tun lokacin da Alpha Conde ya zama zababben shugaba na farko a tarihin kasar Guinea a karshen shekarar 2010, ya taba nada Fofana a matsayin firaminista.
Mohamed Fofana mai shekaru 62 a duniya, ya kasance wani shahararren masani a fannin tattalin arziki na kasar Guinea, wanda ya taba aiki a ma'aikatar kasuwanci, da sauran sassan gwamnatin kasar Guinea daban daban. Kuma zai gabatar da sabbin sunayen ministocin da yake son nadawa idan shugaba Conde ya amince da su a 'yan kwanaki masu zuwa. (Bello Wang)