in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar Ebola ta kashe mutane 59 a kasar Guinea
2014-03-24 15:29:06 cri

Kasar Guinea da ke yammacin Afirka ta tabbatar a ran 23 ga wata cewa, cutar Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 59 a kasar kuma mai yiyuwa ne wannan cuta ta kara bazuwa a yankunan da ke makwabtaka da kasar.

An riga an kaddamar da ayyukan yin rigakafi da aikin ceto don yaki da cutar Ebola a yammacin Afirka. Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Guinea ta bayyana cewa, bisa taimakon kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, hukumomin likitanci na Guinea suna iyakacin kokari domin shawo kan wannan cuta. Ban da wannan kuma, Kungiyar likitocin ta kasa da kasa wato 'Doctors Without Borders' ta sanar da cewa, wata tawagar likitanci da ke kunshe da mutane 24, ciki har da likitoci, da nas-nas, da kuma kwararru da ke nazarin cututtuka masu yaduwa ta tashi zuwa yankunan da ake fama da cutar Ebola a kasar Guinea. Kafin haka kuma, jiragen saman jigila guda biyu da ke dauke da na'urorin musamman da magunguna da nauyinsu ya kai ton 33 sun tashi daga Belgium da Faransa bi da bi, zuwa Guinea, don gudanar da aikin ceto.

Yanzu ba a sani ba ko za a iya shawo kan cutar Ebola a Guinea ko a'a, amma cutar tana kara yaduwa a yammacin Afirka. Kungiyar WHO ta nuna cewa, yanzu a bakin iyaka da ke tsakanin Saliyo da Guinea, an gano wata cuta da ake shakkar cutar Ebola ce, wani yanki na daban da ake ganin zai fi saukin gamuwa da cutar shi ne kasar Liberia da ke makwabtaka da Guinea. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China