in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Guinea ta ki yarda Belgium ta yi hayar jirginta sama na soja wajen dawo da 'yan kasar Guinea da ba su da takardu
2014-03-19 10:27:48 cri

Gwamnatin kasar Guinea ta tabbatar a ran 18 ga wata cewa, kasar ta ki yarda Belgium ta dawo da 'yan kasar Guinea 27 da ba su da takardu, gwamnatin ta yanke shawarar cewa, ba za ta amince da kasashen wajen da su gabatar mata da bukatar hayar jiragen samanta don dawo da 'yan kasar da ba su da takardu ba.

Bisa matsayin da gwamnatocin Belgium da Guinea suka cimma a gun shawarwarin da suka yi, Belgium za ta yi hayar wani jirgin saman soja don ya yi jigilar 'yan kasar Guinea 27 da ba su da takardu daga Belgium zuwa Guinea, amma Guinea ta canza ra'ayinta a karshe, kuma ta haramta wa jirgin saman sojan ya sauka a kasar, wannan ya tilastawa Belgium ta dakatar da wannan shiri.

Ministan harkokin wajen kasar Guinea François Fall ya amince da wannan lamari. A ganinsa, hayar jirgin sama don dawo da 'yan kasar za ta kawo babbar illa, tare da bata sunanta, sakamakon haka ne gwamnatin ta ki yarda da wannan shiri. Ya kara da cewa, a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, gwamnatin Guinea za ta tura wata tawagar manyan jami'ai zuwa Belgium, domin yin shawarwari da kasar kan yadda za a dawo da 'yan kama wurin zauna 'yan kasar ta Guinea da ke zaune a kasar Belgium ba bisa doka ba. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China