Shugaban wucin gadi na kasar Guinea-Bissau Manuel Serifo Nhamadjo ya sanar a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 3 ga wata cewa, ba zai shiga babban zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 13 ga watan Afrilu ba.
Nhamadjo ya bayyana cewa, ba zai zama dalilin rashin zaman lafiya a kasar ba, sabo da ba zai shiga babban zaben shugaban kasar a matsayin 'dan takara ba. Ya ci gaba da cewa, an taba neman shi da ya shiga babban zaben, amma ya ki yarda da gayyatar bisa girmamawarsa ga dokoki da alkawarin da ya yi a baya.
A ranar 12 ga watan Afrilun shekara ta 2012 ne, aka yi juyin mulkin soja a kasar Guinea-Bissau. A kuma watan Mayu na wannan shekarar, aka kafa gwamnatin wucin gadi a kasar bisa matsin lambar kasashen duniya, bayan haka ne kuma, jam'iyyu, da kungiyoyi, da sojojin kasar suka yanke shawarar cewa, shugaban wucin gadi da firaministan wucin gadi ba su da ikon shiga babban zabe da za a gudanar bayan wa'adin aikin gwamnati mai ci.(Danladi)