Garambawul din ya karkata kan mutanen dake rike da manyan mukaman da shafi tattalin arziki da raya zaman al'umma, daga cikinsu akwai tsohon ministan tattalin arziki da kudin kasar Kerfalla Yansane da aka nada ministan ma'adinai da albarkatun kasa, tsohon ministan kasafin kudin kasar Mohamed DIARE ya zama ministan tattalin arziki da kudin kasar. Haka kuma, an nada sabbin ministocin gine-gine da sufuri da kuma na makamashin kasar.
Akasarin mambobin sabuwar gwamnatin da aka nada sun kasance na hannun damar Conde ko 'ya'yan RPG jam'iyya mai mulki, babu guda da ya fito daga jam'iyyar adawa ta kasar.
A ranar 13 ga wata, an kafa sabuwar majalisar dokokin kasar Guinea. Sa'an nan, firaministan kasar Mohamed Saïd Fofana da sauran mambonin gwamnatin sun yi murabus, don kafa sabuwar gwamnatin. A ranar 18 ga wata, Conde ya sake nada Fofana a matsayin firaministan domin kafa sabuwar gwamnatin kasar.(Bako)