Najeriya na fama da ayyukan ta'adanci dake da hannun 'yan kishin islama na kungiyar Boko Haram wadanda suka janyo mutuwar mutane fiye da dubu daya da dari biyar, wadanda yawancinsu mata da yara tun daga bakin shekarar 2009.
Shugaba Jonathan ya jaddada a yayin wannan biki cewa sabbin hafsoshin ya kamata su gudanar da muhimmin aiki wajen kawo sauyi ga rundunar sojojin Najeriya bisa tsarin da ya shafi sauye sauyenta.
Haka kuma ya bayyana cewa hukumarsa ta dauki niyyar bunkasa harkokin tsaro da shari'a, tare da gayyatar wadannan sabbin hafsoshin da suka gama karatu da su yi amfani da ilmin da suka samu wajen kawo sauyin cikin aikinsu. (Maman Ada)