A yayin da yake ba da sanarwar, kakakin rundunar sojojin Najeriyar Mohammed Dole, ya ce, an yi amfani da jiragen saman yaki, don kai hari ga wata makarfafar 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram, inda aka kashe dakarun kungiyar 74, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka.
A cewar Dole, sojojin gwamnati 2 ne suka ji rauni yayin wannan sumame, ba kuma a samu wani rahoto na rasa rayuka, ko jikkatar fararen hula ba.
Tun dai cikin watan Mayun wannan shekara ne shugaban kasar Najeriyar Goodluck Jonathan, ya sanar da kafa dokar ta-baci a jihohin Borno, da Yobe, da Adamawa, dake arewa maso gabashin kasar. Aka kuma jibge sojoji da dama a wadannan yankuna, don dakile ayyukan dakaru masu dauke da makamai dake goyon bayan kungiyar ta Boko Haram. (Bello Wang)