An kai ma kwalejin ilimin aikin gona dake Gujba mai nisan kilo 50 daga Damaturu babban birnin jihar Yobe harin ne lokacin da wassu 'yan bindiga suka fara harbi ta ko ina, abin da ya yi sanadiyar harbe dalibai da dama har lahira.
Wata majiya ta shaida ma wakilin Xinhua cewa an samu gawawwaki da dama a cikin dazukan kewayen makarantar, dakunan daukar darasi da kuma dakunan kwana daliban dake ciki da wajen makarantar, kuma har a lokacin da labarin ya iso mana nan, majiyar ta tabbatar da ana kan tsinto wassu gawawwakin da kuma ceto wadanda suka ji rauni.
Jami'an tsaro dai ba su kai ga tabbatar da labarin ba ko kuma adadin wadanda wannan harin ya rutsa da su a lokacin da labarin ya iso mana. (Fatimah Jibril)