Wani jami'in kasar India ya bayyana a ranar Laraba 19 ga wata cewa, kasarsa ta kaddamar da sabon shirin laluben jirgin saman Malaysian nan da ya bace, cikin sabon shirin na kasar Malaysia, inda kasar ta bukaci kasar India da ta gudanar da aikin bincike a yankin kudancin tekun India. Kuma jiragen saman kasar guda biyu za su tashi daga sansanonin jihar Tamil Nadu na kudancin kasar da kuma tsibirin Andaman na kasar don gudanar da aikin ta sama.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, aikin laluben jirgin saman Malaysian ya kasance wani babban aiki ga kasar Amurka, kuma kasar na amfani da dukkan hanyoyin da take da su don taimaka wa kasar Malaysia dangane da wannan aiki. Kuma wannan shi ne karo na farko da shugaba Barack Obama ya bayyana ra'ayinsa kan wannan harka ta talebijin, tun bacewar jirgin saman na kasar Malaysia (Maryam)