in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano wasu abubuwa da ka iya zama tarkacen jirgin saman Malaysia ne da ya bace, in ji jami'in Australia
2014-03-20 15:47:50 cri
A yau Alhamis 20 ga wata ne, wani jami'in hukumar tsaron tekun kasar Australia ya bayyana cewa, kasarsa ta gano wasu abubuwa a kudancin tekun Indiya da ka iya zama tarkacen jirgin saman Malaysia da ya bace, kuma kasar ta riga ta aike da jiragen sama da jiragen ruwa zuwa yankin tekun da abin ya shafa, don tabbatar da lamarin, da kuma gudanar da aikin bincike.

Sa'an nan kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, labarin da kasar Australia ta samar ya janyo hankalin kasar Sin sosai, kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Australia da ya yi tattauna tare da bangaren Australia, don taimaka wa kasar wajen gudanar da aikin bincken yadda ya kamata, kuma kasar Sin za ta shirya ayyukanta da abin ya shafa dangane da ko wane irin sabon ci gaba da za a iya samu dangane da batun. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China