in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Rasha ya amince da 'yancin kai na Crimea a hukunce
2014-03-18 10:28:37 cri

Jiya Litinin 17 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sa hannu kan dokar da ta amince da  Crimea da ta kasance wata kasa mai 'yancin kai kuma mai cikakken iko

Bisa labarin da aka samu daga shafin Intanet na shugaban kasar Rasha, an ce, dokar da shugaba Putin ya sa hannu ta bayyana cewa, kasar Rasha ta amince da 'yancin kai da mulkin kai na kasar Crimea, bisa aniyar da jama'ar kasar suka nuna a yayin kuri'ar raba gardama da kasar Crimea ta kada a ran 16 ga watan Maris. Kuma dokar za ta fara aiki ne tun lokacin da shugaba Putin ya sanya hannu a kai.

A ranar Lahadi 16 ga wata ne, aka kada kuri'ar raba gardama game da makomar yankin a jamhuriyar Crimea mai cin gashin kanta na kasar Ukraine. Sa'an nan kuma, sakamakon da aka samu,ya nuna cewa, sama da kasha 96 bisa 100 na jama'ar yankin ne suka nuna amincewa da komawar yankin na Crimea kasar Rasha.

A ranar Litinin 17 ga wata, majalisar dokokin jamhuriyar Crimea mai cin gashin kanta ta tsai da da shawara cewa, Crimea ta kasance kasa mai 'yancin kai kuma mai mulkin kai, kuma sunanta yanzu shi ne jamhuriyar kasar Crimea. Bugu da kari, majalisar dokokin kasar ta gabatar wa kasar Rasha wasu shawarwari, inda ta nuna cewa, tana son shiga tarayyar Rasha a matsayin yanki mai cin gashin kansa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China