in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burin kasar Sin ya fi na Amurka janyo hankulan kasa da kasa
2014-03-21 15:45:53 cri

Kwanan baya, kamfanin tallace-tallace da watsa labarai na WWP na kasar Burtaniya, ya fidda da wani rahoto mai taken "Tasiri da muhimmancin burin ci gaba na Sinawa" a majalisar walilai na kasar, wanda ya nuna cewa, duk da gajartar lokacin da kasar Sin da fitar da manufarta ta cigaba, Burin nata ya dara na kasar Amurka janyo hakulan kasa da kasa.

Kamfanin WWP ya fitar da rahoton ne bayan wani bincike da ya yi kan karbuwar wasu kamfanoni ko masana'antun kasar ta Sin, tsakanin 29 ga watan Satumba zuwa 15 ga watan Oktobar bara, inda ya zabi wakilai guda 500, daga kasashen Birtaniya, Sin da Amurka, don su amsa tambayoyi game da wannan batu ta kafar yanar gizo, cikin mintuna 25.

Sakamakon hakan, rahoton ya nuna cewa, Sinawa suna mai da hankali kan farin cikin iyalansu, da kuma bunkasuwar kasarsu, yawan mutanen da suka fahimci babban burin kasa a kasar Sin ya kai kaso 92 bisa dari, da kaso 81 bisa dari a Amurka, sai kuma kaso 10 bisa dari a Burtaniya.

Har wa yau bisa rahoton da kamfanin na WWP ya fitar, an ce, wadanda aka yiwa tambayoyin a intanet a kasashen uku suna da imanin cewa, kasar Sin na da makoma mai kyau, kuma adadin mutanen dake da ra'ayin cewa kasar ta Sin za ta kasance kasa mafi samun bunkasuwa, ya yi daidai da na wadanda ke dauke da ra'ayin cewa, kasar Amurka za ta kasance kasa mafi samun bunkasuwa tsakanin kasashen duniya.

A kasar Amurka, mutane sama da kashi daya bisa hudu na ganin cewa, kasar Sin za ta kasance kasa mafi samun bunkasuwa a nan gaba, kana a kasar Burtaniya, galibin jama'ar kasar na ganin cewa, a halin yanzu, kasar Amurka ita ce kasa mafi samun bunkasuwa tsakanin kasashen duniya, ko da yake kasar Sin za ta maye gurbinta a nan gaba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China