in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya yi kira da a ci gaba da taron Geneva
2014-03-15 17:27:10 cri
Jiya Jumma'a 14 ga wata, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, yunkurin warware rikicin siyasar kasar Syria, ya shiga wani yanayi na tabarbarewa, don haka ya yi kira ga kasashen Amurka, da Rasha, wadanda su ne suka assasa taron Geneva tun da farko, da su dauki matakai na ci gaba da yankurin warware wannan batu ta hanyar siyasa.

Bugu da kari, bayan wani kwarya-kwaryan taro kan batun kasar ta Syria karo na 68, da babban taron MDD ya gudanar a wannan rana, Mr. Ban ya bayyana wa kafofin watsa labaru cewa, bayan kammala taron shawarwari a zagaye na biyu, bangarori biyu da batun Syria ya shafa, watau gwamantin kasar Syria da tsagin 'yan adawar kasar ba su nuna wata himmar yin hadin gwiwa ba.

Haka kuma, bangarorin biyu sun ki yin la'akari da wahalhalun da jama'ar kasar ke fuskanta. Don haka ne Mr. Ban ya bukaci daukacin bangarorin da wannan batu ya shafa da su dakatar da fadace-fadace tsakaninsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China