A wannan rana, yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi maraba sosai kan wannan kuduri da ke nuna fata da bukatar gamayyar kasa da kasa sosai game da kyautata yanayin jin kai na kasar Syria. Kasar Sin ta kada kuri'ar amincewa a yayin kada kuri'u.
Mr. Qin ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana fatan bangarorin biyu da abin ya shafa na kasar Syria da su ci gaba da shawarwarin dake tsakaninsu, tare da nuna goyon baya da girmama kokarin da wakilin musannan na MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa kan batun Syria Lakhdar Brahimi ya yi, kana su ci gaba da shawarwarin dake tsakaninsu, har sai sun cimma sakamako mai gamsarwa. (Maryam)