MDD da kungiyon jin kai sun shirya kai abinci, magunguna da sauran kayayyaki a kusa da Homs, domin isar da su cikin garin da zaran bangarorin sun amince bude hanya mai tsaro, in ji wannan sanarwar da mataimakin kakakin MDD, Farhan Haq ya karanta.
Haka kuma ya bayyana cewa, Valerie Amos dake kula da harkokin jin kai na MDD, ita ma ta nuna gamsuwarta kan wannan labari na samun sararin kai taimako a birnin Homs, da kuma zai taimakawa fararen hula ficewa daga garin, da kuma kai kayayyakin bukatun yau da kullum ga mutane fiye da dubu biyu da dari biyar.
Madam Amos, mataimakiyar sakatare janar kan harkokin jin kai ta MDD, kuma mai kula da ayyukan agajin gaggawa za ta ci gaba da sanya ido kan halin da ake cike a kasar ta Syria, in ji mista Haq. (Maman Ada)