Brahimi ya bayyana cewa, sassan biyu sun dauki lokaci mai tsawo suna tattaunawa, inda aka tabo muhimmin batu, wato yanayin tsaro a Syria da kuma batun ayyukan ta'addanci wanda aka amince cewa, akwai shi kuma wata babbar matsala ce da ake fuskanta a cikin kasar ta Syria, amma ba a cimma wata matsaya ba game da yadda za a magance wannan matsala.
Brahimi ya ce, sanin kowa ne cewa, muddin ana bukatar warware matsala tare da samun zaman lafiya da tsaro a Syria, tilas sai an magance matsalar tsaro da farko.(Ibrahim)