Brahimi ya shaidawa taron manema labarai cewa, taron na wannan zagaye na da matukar wahala kana babu ci gaban a zo a gani, amma daga karshe sassan biyu sun saba zama da juna a daki guda, tare da nuna sanin ya kamata yayin tattaunawar.
A cewarsa, sassan biyu sun tattauna bisa shiga tsakaninsa kan halin da ake ciki a halin yanzu a kasar da yaki ya daidaita da kuma yankin Homs da aka mamaye.
Brahimi ya ce, cikin abubuwan da suka tattauna, sun hada da batun tsagaita bude wuta daga dukkan fannoni, yaki da ayyukan ta'addanci da kafa gwamnacin wucin gadi mai cikakken iko, sai dai akwai bambancin ra'ayi tsakanin sassan biyu kan wadannan batutuwa.
Jami'in ya bayar da shawarar gudanar da zagaye na gaba na shawarwarin ranar 10 ga watan Fabrairu, wadda ta samu amincewar bangaren 'yan adawa, yayin da wakilan gwamnati suka ce, suna bukatar su tattauna da fadar shugaban kasa da farko. (Ibrahim)