in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An lalata kashi daya bisa uku na makamai masu gubar Syria
2014-03-06 11:20:07 cri
Mai shiga tsakani na musamman na tawagar hadin gwiwar MDD da kungiyar kula da harkokin haramta makamai masu guba Sigrid Kagg, ta ce kawo yanzu an riga an lalata kashi daya bisa uku, na wadannan makamai, kuma mai iyuwa ne a kai ga lalata daukacin su nan da karshen watan Yuni mai zuwa. Kagg ta bayyana hakan ne a jiya Laraba 5 ga watan nan na Maris.

A kuma dai wannan rana, kwamitin kasa da kasa mai binciken batutuwan da suka shafi kasar ta Siriya na MDD, ya bayyana a birnin Geneva cewa, yawan fararen hula dake fuskantar barazana daga dakarun gwamnati da na 'yan adawa sun kai dubu 250.

Kwamitin ya kara da cewa, baya ga barazana ga rayuwarsu, wadannan fararen hula na kuma huskantar karancin abinci, da ababen bukata na yau da kullum, da karancin tsarin kula da lafiya, da kuma rashin samun taimakon jin kai. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China