kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Qin Gang ya bayyana a nan birnin Beijing lokacin taron manema labarai inda yace a don haka kasar na fatan bangarorin da batun Ukraine ya shafa ba za su dauki matakan da za su tsananta yanayin da ake ciki ba.
An bada labarin cewa, a ranar alhamis, majalisar dokokin yankin Crimea mai cin gashin kanta ta sanar da cewa zata shirya jefa kuri'ar raba gardama kan ko za ta shiga tarayyar Rasha cikin kwanaki 10 masu zuwa abinda kasar Amurka da kungiyar tarayyar kasashen Turai suke ganin hakan ya keta dokar kasa da kasa.
Dangane da hakan mista Qin ya ce kasar Sin na kira ga bangarori daban daban na Ukraine da su daidaita matsala ta hanyar yin shawarwari cikin lumana kuma bisa dokoki, a kokarin kiyaye kare iko da moriyar jama'ar kasar, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin lokaciyankunan da batun ya shafa.(Fatima)